Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-28 15:37:31    
Bunkasuwar kauyukan lardin Jiangsu na kasar Sin

cri

Lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin yana daya daga cikin yankuna da aka samu sakamako mai kyau wajen raya kauyuka.

An kafa yankin masana'antu a karkarar birnin Suzhou na lardin Jiangsu ne bisa yarjejeniyar hadin guiwa da aka daddale tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Singapore. Yanzu ana sarrafa kayayyakin sadarwa da na'urori masu inganci da magunguna da aka yi da abubuwa masu rai da kayayyaki irin na sabon salo da sauransu a wannan yankin masana'antu. Madam Yao Wenlei, mataimakiyar shugabar ofishin hukumar kula da wannan yankin masana'antu ta bayyana wa wakilinmu cewa, yayin da ake raya yankin masana'antun nan, an gaggauta raya kananan garuruwa iri na zamani a karkarar birnin Suzhou. Ta ce, "yanzu, kashi 90 cikin dari na manoma suna kwana a cikin unguwannin gidajen kwana irin na zamani. Ana bai wa manoma tsoffafi kudin fenso don ciyar da su. A sa'i daya kuma ana horar da manoma samari don su sami aikin yi a masana'antu. Hukumar yankin ta kan kashe kudi mai yawa don tallafa wa manoma da ke fama da talauci, ta yadda za a taimake su wajen kubutar da su daga talauci. "

Bayan da aka mayar da kauyuka da yawa na lardin Jiangsu da su zama yankin bunkasuwar tattalin arziki ko yankin masana'antu, sai manoma da ke zama a wadannan yankuna suka sauya tsabi'un zaman rayuwarsu, sun fara zamansu irin na sabon salo.(Halilu)


1  2  3