Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-28 15:37:31    
Bunkasuwar kauyukan lardin Jiangsu na kasar Sin

cri

A yayin da ake neman canja irin wannan hali da ake ciki, an mayar da wani kogi mai suna "Guan" da ya ratsa gundumar don ya zama albarkatu da ake iya amfani da shi wajen raya gundumar. Wannan kogi yana da fadi da zurfi, inda jiragen ruwa ke iya kai da kawowa cikin sauki. Sa'an nan kuma yana hade da bakin teku mai tsawon kilomita sama da 160, da kwata mai zurfi sosai. Sabo da haka hukumar wannan gunduma ta yanke shawara a kan kafa wani yankin bunkasa tattalin arziki bisa matsayi mai rinjaye na saukin jigilar kayayyaki da arahar kwadago.

Bayan da aka shigad da makudan kudaden jari da aka zuba wajen kafa masana'antu da yawa a yankin bunkasa tattalin arziki na gundumar "Guan", an daga matsayin tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a na gundumar. Yanzu manoman wannan gunduma da yawa sun riga sun saba da yin aiki cikin masana'antu a lokacin hunturu da ba a zuwa aikin gona.

Madam Xiao Hongxia manomiya ce a da wadda yanzu ke aiki a wata masakar tufafi ta yankin nan ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa, "yau da shekaru uku da suka wuce, na taba yin aiki a kasar Japan. Bayan da na dawo gida daga kasar Japan, sai na sami aikin yi a wannan masakar tufafi. Ta kara da cewa, "ko da yake yawan albashi da nake samu bai kai na kasar Japan ba, amma na fi sabawa da zamana a gundumarmu. Yanzu ana kula da masakarmu daidai yadda ake yi a kasar Japan. A da a lokacin aiki, ma'aikata su kan yi magana da yawa yadda suka ga dama, amma yanzu ba su yin haka."


1  2  3