Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-28 15:37:31    
Bunkasuwar kauyukan lardin Jiangsu na kasar Sin

cri

Kasar Sin wata babbar kasa ce ta aikin noma. Tattalin arziki da zaman jama'a na kauyuka na kasar suna baya-baya, idan an kwatanta su da na birane har cikin wani tsawon lokaci. Don neman canja irin wannan hali da ake ciki, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gabatar da manufar gaggauta raya kauyuka nan da shekaru 5 masu zuwa.

Da farko, wakilin gidan rediyonmu ya kai ziyara a gundumar da ake kira "Guannan" cikin Sinanci da ke arewacin lardin Jiangsu. Wannan gunduma na shimfide ne a wani falalin fili da ba hawa da sauka, kuma nan ne sansanin noman auduga mai inganci a kasar Sin, amma ana bunkasa harkokin tattalin arzikinta sannu sannu. Malam Sun Ming, jami'in gundumar nan ya bayyana wa wakilinmu cewa, babban dalili da ya sa ba a iya bunkasa harkokin tattalin arzikin gundumar da sauri shi ne, domin ana mai da hankali sosai ga aikin noma fiye da harkokin kasuwanci. Ya ce, "harkokin tattalin arzikin gundunarmu mai suna "Guannan" suna baya-baya sosai har cikin wani tsawon lokaci da ya wuce. Yawan kudin jari da 'yan kasuwa na kasashen waje suka zuba a gundumarmu da matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane manomi ya samu da kuma matsakaicin yawan albashi da ko wane ma'aikaci ya samu duk ya kai matsayin kurya a duk lardin Jiangsu gaba daya a shekarar 2002."


1  2  3