Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 16:12:35    
Sin tana inganta manufofinta game da kayyade yawan kudin jari da kasashen waje ke zubawa a kasuwannin gidaje

cri

Masanan ilmi da yawa sun nuna ra'ayinsu daidai da Malam Yi Xianrong. Sun nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta fitar da sabbin manufofin nan ne ba don hana baki na kasashen waje su saye gidaje a kasar Sin ba, sai domin hana masu zuba jari na kasashen waje su yi cinikin gidaje a kasar Sin. Sabbin manufofin nan suna dacewa da manufofi da ake gudanarwa a kasashen duniya. Daga cikin kasashe wakilan hukumar ba da lamuni ta duniya wato IMF, akwai su sama da 130 wadanda suka kayyade yawan kudi da masu zuba jari na kasashen waje ke zubawa wajen yin cinikin gidaje.

Madam Dai wadda ke aiki a wani shahararren kamfanin ba da shawara kan harkokin gidaje na duniya ta bayyana cewa, wadannan sabbin manufofin kasar Sin za su taka rawa wajen kayadde yawan kudi da masu zuba jari na kasashen waje ke kashewa wajen yin cinikin gidaje a kasar Sin. Ta ce, "makasudin sabbin manufofin gwamnatin kasar Sin shi ne domin neman masu zuba jari na kasashen waje da su zuba jari a kasuwannin gidaje na kasar Sin yadda ya kamata. Nan gaba kuma kamfanonin zuba jari na kasashen waje da 'yan kasuwa masu zaman kansu ba za su iya kashe makudan kudade ba ji ba gani wajen sayen gidaje kai tsaye a kasar Sin ba." (Halilu)


1  2  3