Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 16:12:35    
Sin tana inganta manufofinta game da kayyade yawan kudin jari da kasashen waje ke zubawa a kasuwannin gidaje

cri

Shekaran jiya ran 24 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da sabbin manufofinta game da kayyade yawan kudin jari da kamfonin kasashen waje da mutanensu masu zaman kansu ke zubawa a kasuwannin gidaje na kasar. Kwararru da abin ya shafa sun nuna cewa, makasudin sabbin manufofin nan shi ne domin hana masu zuba jari na kasashen waje su kara farashin gidaje a kasar Sin, kuma sun kyautata zaton cewa, yawan kudi da ake kashewa wajen yin cinikin gidaje zai ragu a wasu wurare na kasar Sin, ka zalika saurin karuwar farashin gidaje ma zai ragu.

Malam Johnson Bruce, dan kasar Britaniya wanda ya shafe shekaru sama da goma yana zaune a kasar Sin, kuma yana aiki ne domin daya daga cikin kafofin watsa labaru na kasar Sin a yanzu. Yana ganin cewa, wajibi ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofinta don kayyade yawan gidaje da baki na kasashen ketare ke saye a kasar Sin. Ya ce, "Sinawa masu dimbin yawa suna gunaguni cewa, ba su da isasshen kudi wajen sayen gidaje, saboda farashin gidaje ya yi yawa. A sa'i daya kuma baki da yawa na kasashen ketare suna sayen gidaje don cin riba a kasar Sin. Idan an tsaida manufa cewa, baki na kasashen waje su iya sayan gidajen kwana domin kansu kawai, to, mai yiwuwa ne za a hana a cin riba daga wajen cinikin gidaje."


1  2  3