Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 16:12:35    
Sin tana inganta manufofinta game da kayyade yawan kudin jari da kasashen waje ke zubawa a kasuwannin gidaje

cri

Ko da yake yawan kudi da masu zuba jari na kasashen waje ke kashewa wajen sayen gidaje a kasar Sin a ko wace shekara bai yi yawa ba, idan an kwatanta shi da jimlar kudade da ake kashewa a wannan fanni, amma yawan kudin nan ya sa farashin gidaje ya kara tashi a manyan birane na Beijing da Shanghai da Shenzhen da sauransu. Dalilin da ya sa haka shi ne domin masu zuba jari na kasashen waje sukan kashe yawancin kudadensu wajejn sayen gidaje a wadannan manyan birane na kasar Sin. Malam Yi Xianrong, shahararren masanin ilmin tattalin arziki na kasar Sin yana nuna goyon bayansa ga sabbin manufofi da gwamnatin kasar Sin ta fitar. Ya ce,"a hakika dai, masu zuba jari na kasashen waje suna taka rawa wajen kara daga farashin gidaje a kasar Sin musamman a biranen Shanghai da Shenzhen. Babban makasudin sabbin manufofin da gwamantin kasar Sin ta fitar shi ne domin kayyade yawan kudi da suke zubawa a kasuwannin gidaje na kasar Sin."


1  2  3