![]( /mmsource/images/2006/07/26/tennis3.jpg)
Mr. Jiang Hongwei shi ma ya fadi albarkacinsa, cewa bayan da aka yi cudanya cikin shekaru da dama tsakanin 'yan wasa da kuma 'yan kallo, na ga 'yan kallon sun samu fahimta sosai game da wasan kwallon tennis, kuma sukan nuna halin da'a lokacin da suke kallon gasa. Ya kuma kara da, cewa : ' Gasar nan da ake yi a wannan gami, wata gasa ce da ta fi samun nasara a cikin gasannin da kasar Sin ta taba daukar nauyin bakuncinsu a da. Mun tuna da cewa, a da, wassu mutane sun ce wai mutanen kasar Sin sun kasa samun ilmi a fannin kallon wasan kwallon tennis, amma yanzu ba haka ba ne.'
A ran17 ga watan da muke ciki, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tenni na sana'a na mata ta kasa da kasa wato WTA ta kaddamar da sunayen jerin 'yan wasa dake bisa matsayin gurabe na farko a duniya.An ciyar da 'yar wasa Li Na ta kasar Sin gaba zuwa matsayin gurabe 15 na farko a duniya a fannin irin wasa tsakanin mace da mace ; kuma Miss.Zhenjie tana bisa matsayin gurabe 29 na farko a duniya.
Yanzu 'yan wasa mata na kasar Sin suna himmantuwa wajen horaswa domin yin marahabin da zuwan budaddiyar gasa ta wasan kwallon tennis da za a yi a watan gobe a kasar Amurka. ( Sani Wang ) 1 2 3
|