Aminai makaunatai, mun yi farin ciki matuka da gaya muku, cewa a ran 9 ga watan nan, 'yan wasa mata su Zhenjie da Yanzi sun samu lambar zinariya a gun budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta Australiya, kuma 'yar wasa mai suna Li Na ta kafa tarihi har ta shiga jerin 'yan wasa guda 4 masu karfi a gun gasar. Ban da wannan kuma, 'yan wasa mata na kwallon tennis na kasar Sin sun sake kafa tarihi a lokacin da bai kai rabin wata ba, wato ke nan sun lallasa 'yan wasan kasar Jamus da ci hudu da daya a gun karin gasa ta kungiyar kasa da kasa ta cin kofin Rederation ta shekarar 2006 wadda aka kawo karshenta a ran 16 ga watan nan, wato ke nan sau na farko ne suka shiga cikin jerin kungiyoyi guda 8 masu karfi na kungiyar duniya na cin kofin Federation.
Tun daga ran 15 zuwa ran 16 ga watan nan, an yi karin gasa ta kungiyar duniya ta cin kofin Rederation ta shekarar 2006 a nan Beijing. Kungiyar kasar Sin ta kara da tsohuwar kasaitacciyar kungiyar kasar Jamus. Kafin wannan lokaci, sun taba yin karawa tsakaninsu har sau biyu, inda 'yan wasa mata na kasar Sin suka sha kaye daga 'yan wasan kasar Jamus. Amma, a gasanni biyu da aka yi a ran 15 ga wata, 'yan wasa Li Na da Zhenjie na kasar Sin kowanensu ya lashe abokiyar karawarsa ta Jamus da ci biyu da ba ko daya; kuma a gasar da aka yi a kashegari, ' yar wasa Li Na ta lallasa abokiyar karawarta mai suna Kathrin Woerle ta kasar da ci 7 da 5, wato ke nan kungiyar kasar Sin ta riga ta samu tikitin shiga gasa ta sabon zagaye. Babban mai koyar da 'yan wasa mata na kasar Sin Mr. Jiang Hongwei ya yaba wa 'yan wasansa sosai, cewa:
' Na gamsu sosai da ganin yadda 'yan wasa mata na kasar Sin suka nuna rawar gani a gun gasar. Musamman ma yadda ' yar wasa Li Na ta yi fintinkau a gun gasar ko da yake tana kamuwa da ciwon ido; kuma 'yar wasa Zhenjie ita ma ta burge ni kwarai da gaske saboda ta ji rauni a jikinta amma a karshe dai ta haye wahalar da take sha har ta samu nasara a gun gasar'.
1 2 3
|