Jama'a masu sauraro, kuna sane da, cewa gasar wasan kwallon tennis ta cin kofin Rederation da akan shirya sau daya a kowace shekara, wata gagarumar gasa ce dake kan matsayin ci gaba a duniya a fannin wasa da aka yi tsakanin kungiya-kungiya na mata. Ra'ayoyin bainal jama'a na kasa da kasa sun yi hasashen, cewa babu tantama, harkar wasan kwallon tennis na mata ta kasar Sin ta shiga wani sabon mataki bayan da ta yi alfarmar shiga cikin jerin kungiyoyi guda 8 masu karfi na kungiyar duniya da aka yi a wannan gami. Ban da kungiyar kasar Sin, sauran kungiyoyi guda 7 su ne: kungiyar kasaar Belgium, da kungiyar kasar Italiya, da kungiyar kasar Spain, da kungiyar kasar Amurka, da kungiyar kasar Rasha, da kungiyar kasar Japan da kuma kungiyar kasar Faransa. A karshen shekarar da muke ciki za a yi bikin kada kuri'a domin tsaida kungiyar wata kasa da za ta kara da kungiyar kasar Sin a cikin gasa ta sabon zagaye da za a yi.
Yanzu, mutane da yawa suna masu sha'awar wasan kwallon tennis a kasar Sin sakamakon kyakkyawan tasirin nasarorin da 'yan wasan kwallon tennis na kasar Sin suka samu. ' yar wasa mai suna Li Na ta yi farin ciki da fadin, cewa: ' Lallai nasarorin da 'yan wasan kasar Sin suka samu suna da nasaba da sa kaimi da 'yan kallon dake filin wasan suka yi.'
1 2 3
|