Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 14:32:08    
Liu Xiang ya karya matsayin bajinta na duniya da aka samar da shi a shekaru 13 da suka wuce

cri

Mr. Sun Haiping ya kara da cewa, makasudi na karshe na Liu Xiang shi ne sake samun lambar zinare a gun taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, ya taba samun lambar zinare a gun taron wasannin Olympic na Athens na shekarar 2004 da dakika 12.91. A lokacin da yake shara fage, babban aikinsa shi ne kyautata halin da yake ciki, da kuma rike da karfinsa, a da bai yi shirin karya matsayin bajinta na duniya a gun wata gasa ba. Ya ce,'A zahiri kuma, ko kusa ba mu yi shirin karya matsayin bajinta a wani lokacin da aka tsai da ba, mai yiwuwa ne za mu nuna rawar gani, za mu karya matsayin bajinta a gun wata gasa. Liu Xiang ya ji rauni a kafarsa, shi ya sa bai yi horo ba har tsawon kwanaki misalin 80. Mun samar da wata hanyar horo daban, wato mu kyautata karfinsa ta hanyar yin horo da yawa a fannin jiki. Sa'an nan kuma, mun share fage ga wadannan gasanni 2. Ko da yake ba mu yi la'akari da karya matsayin bajinta na duniya ko a'a ba, amma a gaskiya kuma muna son samu maki mai kyau a cikin gasannin da za a yi a wannan shekara.'

Idan an waiwayi gasannin da Liu Xiang ya yi, an gano cewa, Liu Xiang ya sami maki mai kyau da yawa ne a Lausanne na kasar Switzerland, har da karya matsayin bajimta na duniya a wannan gami, ma iya cewa, Lausanne wuri ne da ya kan kawo wa Liu Xiang sa'a. Liu Xiang yana da ra'ayi daya kan wannan, ya ce, 'na kan gwada gwanintata lami lafiya a lokacin da nake yin gasa a Lausanne. Amma da can ban yi tsammanin cewa, zan iya karya matsayin bajimta na duniya ba.'

Ran 13 ga watan Yuli ranar haihuwa ce ta Liu Xiang, a lokacin nan shekarunsa ya kai 23, ko shakka babu karya matsayin bajinta na duniya wata kyauta ce mafi kyau da shi ya ba kansa. Mutane suna fatan cewa, wannan dan wasan kasar Sin saurayi zai kara samun maki mai kyau a nan gaba, zai dinga kawo wa kasar Sin da duniya mamaki da farin ciki. Mutane sun yi imanin cewa, Lausanne wuri ne da ya kan kawo wa Liu Xiang sa'a, amma ba tasha ce ta karshe gare shi ba.(Tasallah)


1  2  3