Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-19 14:32:08    
Liu Xiang ya karya matsayin bajinta na duniya da aka samar da shi a shekaru 13 da suka wuce

cri

Ran 12 ga wata da sassafe bisa agogon Beijing, a gun gasar ba da babbar kyauta ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta shekarar 2006 da aka yi a birnin Lausanne na kasar Switzerland, dan wasan kasar Sin Liu Xiang ya zama zakara da dakika 12.88 a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110, ya kuma karya matsayin bajinta na duniya na dakika 12.91, wanda shahararren dan wasan kasar Birtaniya Colin Jackson ya samar da shi a shekaru 13 da suka wuce.

Dan wasan kasar Amurka Dominique Arnold ya zama na biyu, ya rungumi Liu Xiang don taya murna. Arnold ya kuma karya matsayin bajinta na duniya da dakika 12.90. Ba safai a kan ga 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje 2 suka karya matsayin bajinta na duniya a sa'i daya a cikin gasa daya ba, kuma wannan bai auku a gun gasar ba da babbar kyauta ta Lausanne a da ba. Jim kadan kuma, kafofin yada labaru na wurare daban daban na duniya sun nuna hoton Liu Xiang da aka dauka, wanda yake zaune a kan injin lissafin lokaci da ke nuna sabon matsayin bajinta na duniya.


1  2  3