'
Ban gaskata cewa, ni ne zakara ba! Sai ka ce wani mafarki. Wannan muhimmin lokaci ne a tarihi. Ban yi fintikau sosai ba a gun gasar da aka yi a Paris. Amma a Lausanne, na tashi daga masomi lami lafiya. Na fara kara sauri tun daga shinge na 5.' Liu Xiang ya fadi haka ne bayan gasar.
Lokacin da yake zantawa da kafofin yada labaru na kasar Sin ta hanyar wayar tarho bayan gasar, Mr. Sun Haiping, malamin wasa na Liu Xiang, ya bayyana cewa,'Liu Xiang ya gwada gwanintarsa sosai a gun gasar da aka yi a yau, shi ya sa ya karya matsayin bajinta na duniya. Da ma ta taba cewa, a ganina, bai yi gudu yadda ya kamata a gun gasar da aka yi a Paris ba, amma tabbas ne zai nuna rawar gani a Lausanne. Mun ji gajiya sosai saboda bambancin lokaci daga Beijing zuwa Paris, ba mu yi barci da kyau ba, shi ya sa ba mu kyautata karfinmu ba. Bayan da muka iso Lausanne, mun yi iyakacin kokarin shirya gasa a kwanakin nan, saboda wannan gasa tana da muhimmanci sosai, sa'an nan kuma, Lausanne wuri ne da ya kan kawo wa Liu Xiang sa'a.'
Liu Xiang dan wasan tsalle-tsalle da guje-guje ne mafi nagarta na kasar Sin a yanzu. Ya yi ta karya matsayin bajinta. Tun daga ya kai matsayin bajinta na Asiya da dakika 7.55 a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 60 a gun gasar ba da babbar kyauta ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da aka yi a cikin dakin motsa jiki a shekarar 2002 har zuwa yanzu, Liu Xiang ya sha yin gyare-gyare kan tarihin wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin a cikin shekaru 4 da suka wuce.
1 2 3
|