Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-30 16:07:27    
Kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet da bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet

cri

A cikin shekaru da yawa da suka wuce, kyawawan wuraren halittu na tudun Qinghai-Tibet da al'adun gargajiya da suke kasancewa a tudun Qinghai-Tibet suna jawo hankulan masu yawon shakatawa na kasar Sin da na ketare. Bisa kididdigar da aka yi, a shekara ta 2004, a karo na farko ne yawan masu yawon shakatawa da suka je jihar Tibet ya kai fiye da miliyan 1. Amma domin a da masu yawon shakatawa su kan je jihar Tibet ta hanyoyin mota da jirgin sama kawai, za a kashe kudi da yawa. Mutane da yawa ba su samu damar shiga jihar Tibet ba. Sabo da haka, mutane wadanda suke tafiyar da sana'ar yawon shakatawa su kan fadi cewa "Yanzu an sami saukin zuwa kasashen waje, amma ana da wuyar shiga jihar Tibet." Bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, za ta iya hada fadar Botala ta jihar Tibet da tsohuwar hanya ta Siliki da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Wadannan wurare za su zama sabbin hanyoyin yawon shakatawa da ke jawo hankulan masu yawon shakatawa. An yi hasashen cewa, bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, yawan masu yawon shakatawa da za su je jihar Tibet zai kai miliyan 2 ko miliyan 3 a kowace shekara.

Yanzu, gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta tana tsara shirin raya sana'ar yawon shakatawa da sana'ar kiwon fatauci da dai sauransu.(Sanusi Chen)


1  2  3