Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-30 16:07:27    
Kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet da bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet

cri

A ran 1 ga watan Yuli, za a kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet kwata-kwata. Wannan zai kawo karshen tarihin rashin hanyar dogo a jihar Tibet mai cin gashin kanta. Masana sun bayyana cewa, kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet za ta bayar da muhimmiyar gudummawa ga karuwar tattalin arzikin jihar Tibet, kuma za ta iya tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet cikin hali mai dorewa ba tare da gazawa ba.

Fadin jihar Tibet mai cin gashin kanta ya kai kashi 1 cikin kashi 8 bisa na duk fadin kasar Sin. Amma a cikin dogon lokacin da ya wuce, an hada jihar Tibet da sauran wuraren kasar Sin ta hanyoyin mota da na jirgin sama kawai. Sabo da haka, ba a iya sufurin kayayyaki da yawa da jihar Tibet take bukata ba. Tabarbarewar harkar zirga-zirga ta zama daya daga cikin muhimman batutuwan da ke hana bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet.


1  2  3