Liu Kai, wani masanin da ya kware kan ilmin tattalin arzikin masana'antu a kwalejin kimiyyar zaman al'umma na kasar Sin ya ce, kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet za ta kyautata halin kama baya da ake ciki a fannin zirga-zirgar jihar Tibet. Yana ganin cewa, bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, za ta bayar da gudummawa ga musayar tattalin arzikin jihar Tibet da sauran yankunan kasar Sin da rage kudin yin sufurin kayayyaki da kuma neman bunkasuwar sana'ar yawon shakatawa mai dorewa a jihar. Sannan kuma, za ta ba da gudummawa wajen raya albarkatun kasa da daidaita bambancin da ke kasancewa a tsakanin yankuna daban-daban. An yi hasashen cewa, ya zuwa shekara ta 2010, yawan kayayyakin da za a shigi da fici a jihar Tibet zai kai ton miliyan 2 da dubu dari 8, daga cikinsu, yawan kayayyakin da za a yi sufuri da su ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet zai kai ton miliyan 2 da dubu dari 1.
Sannan kuma, hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, kamar wani injin ba da karfi, za ta ba da gudummawa sosai ga yunkurin raya zaman al'ummar zamani a jihar Tibet. Hanyar dogo ta Qinghai-Tibet za ta hada kasuwar jihar Tibet da kasuwannin sauran yankunan kasar Sin sosai, wannan zai rage yawan kudaden da mutanen jihar Tibet za su kashe domin sayen kayayyakin masarufi da kayayyakin kawo albarka. Mutanen jihar Tibet za su samu moriya kai tsaye daga wannan hanyar dogo. Musamman sana'ar yawon shakatawa a jihar Tibet da sana'ar magungunan Tibet da sana'ar hakar albarkatun kasa da sana'ar sarrafa amfanin gona da naman dabbobi da sauran sana'o'in da ake yi a jihar Tibet kawai za su kama hanyar neman bunkasuwa mai dorewa, kuma za su zama sabbin muhimman sana'o'in da ke ba da taimako ga tattalin arzikin jihar. Bugu da kari kuma, domin wannan hanyar dogo tana hade jihar Tibet da lardin Qinghai, wadannan yankuna biyu za su iya samun bunkasuwa tare.
1 2 3
|