Wakiliyarmu ta ce , A bikin al'adun Olympic na shekarar 2005 da aka yi , wasannin cartoon sun mamaye a kudu maso arewacin kasar Asiya . An kiyasta cewa , ya zuwa karshen wannan shekara yawan wasannin katoon zai kai kusan 100 . Wannan ba a iya ganin saurinsu ba a cikin shekaru biyu da suka shige ba . Ma iya cewa , wasannin kwaikwayon cartoon sun zama sabon salo mai jawo hankulan mutanen Beijing da na kasashen waje kwarai da gaske .
Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da sabon tsarin shirya Wasan Olympic , wannan ba kawai a wajen kimiyya da fasaha ba , har ma a wajen wasanni da al'adu . Yalwatuwar masana'antun wasanni da al'adu a Bikin Wasan Olympic ta sa mutanen kasar Sin suka sauya tsohon tunaninsu kuma ta kawo karin jarumtaka . Mr. Wang Yu , babban manajan kamfanin shirye-shirye na Kwamitin wasan Olympic na Beijing ya ce, nan gaba za mu mai da hankali kwarai a kan ingancin wasannin al'adun.(Ado ) 1 2 3
|