Kwanakin nan a nan Birnin Beijing , hedkwatar Kasar Sin , ana nune-nune wasannin al'adun shahararrun gasanni na kasar Sin da na kasashen waje .
Wasan Olympic wani babban aiki ne na 'dan Adam , Ta hanyar yin aikace-aikacen al'adu , za a sa jama'ar duk kasar Sin da su sami tunanin Wasan Olympic . Duk wadannan sun bayyana kyawawan al'adu masu jawo hankulan mutanen duniya .
Wakiliyar Rediyon kasar Sin ta ruwaito mana labari cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , a nan kasar Sin tana mai da hankali sosai kan sha'anin al'adu da wasanni. Gwamnatocin matakai daban daban suna mai da muhimmanci a kansu . Jama'a na bangarori daban daban suna shiga cikin wannan aikin . Yanzu larduna da jihohi na kashi 2 cikin 3 na duk kasar Sin sun gabatar da cewar za su kafa sha'anin wasannin al'adu da ya zama babbar masana'antarsu . A cikin shirinmu na yau za mu kai ku zuwa Babbar Ganuwa dake arewacin birnin Beijing na kasar Sin don binciken hakikanin abubuwa a wajen yalwata sha'anin wasannin al'adu .
1 2 3
|