Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 16:19:50    
Ziyarar da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a kasashen Afirka ta sami sakamako da yawa

cri

"Huldar da ke tsakanin kasashen Sin Afirka ba ta wucin gadi ba ce, maimakon haka nasarori ne da bangarorin biyu suka samu bayan kokarin da suka yi a shekaru 50 na baya. A taron manema labaru da aka yi a kasar Masar, firaminista Wen Jiabao ya jaddada cewa, an kafa huldar abokantaka tsakanin kasashen Sin da Afirika lokacin da ake yin yaki da mulkin mallaka, kuma kasashen Afirka suna nazarin hanyoyin da kaasr Sin ta bi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki."

Mr. Huang Shejiao ya ce, firaminista Wen Jiabao ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin da Afirka su kara hadin gwiwa bisa samun ka'idar moriyar juna. Ya ce, gwamnatin kasar Sin tana karfafa kwarin gwiwa ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasashen Afirka. Kuma shugabannin kasshen Afirka sunn yin maraba da wannan, bangarorin biyu suna son za su kara matsayin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki.

Mr. Huang Shejiao ya ce,"Bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka tana da dama sosai. Kasar Sin tana cigaba da bunkasa huldar, kuma kasashen Afirka sun san muhimmancin bunkasuwar tattalin arziki don haka suna son su yi hadin gwiwa tare da kasar Sin, ta haka bangarorin biyu za su sami moriyar juna tare."


1  2  3