Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 16:19:50    
Ziyarar da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a kasashen Afirka ta sami sakamako da yawa

cri

Mr. Huang Shejiao ya ce, ziyarar firaminista Wen Jiabao ta sake kara sada zumuncin da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka don kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare tsare ta sabon matsayi bayan shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi ziyara a kasashen Morroco, Nijeriya, Kenya a watan Afrairu na wannan shekara. Huang Shejiao ya ce, dalilan da suka sa shugabannin kasar Sin suka kai ziyara a kasashen Afirka bi da bi su ne, da farko, shekarar da muke ciki wata shekara ce mai muhimmanci, ita "shekarar kasar Sin" ta kasashen Afirka, na biyu kuma wannan ya nuna cewa kasashen Afirka suna da muhimmanci sosai ga kasar Sin.

"Shekarar da muke ciki ita ce shekarar cika shekaru 50 da aka kafa huldar diplomasiya da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka. Don tunawa da wannan al'amari mai muhimmanci, gwamantin kasar Sin ta dauki matakai a jere. A watan Janairu, gwamnatin kasar Sin ta bayar da 'takardar manufofin da kasar Sin take tafiya kan kasashen Afirka'. shugabanni sun yi ta kai ziyara a kasashen Afirka, kuma a watan Nuwanba za a yi taron koli."

Amma, wasu kasashen Turai sun bayar da wasu labari maras sahihanci, sun ce gwamnatin kasar Sin tana tafiyar da "sabon mulkin mallaka" don neman makamashin kasashen Afirka. Mr. Huang Shejiao ya ce, firaminista Wen Jiabao ya bayyana manufofin da kasar Sin take tafiya kan kasashen Afirka a duk fannoni.


1  2  3