
Malam Wang Hongyi yana ganin cewa, bisa ci gaba da ake kara samu wajen kara karfin hadin guiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afrika, jama'ar Afrika za su kara samun fa'ida, don haka ko shakka babu, irin wannan surutun banza na Turai ta yamma zai bi ruwa. Ya ce,"moriyar da Afrika ke samu daga wajen hadin guiwar da ake yi tsakaninta da Sin a fannin makamashi da albarkatun kasa ta fi moriyar da take samu daga wajen hadin guiwar a tsakaninta da kasashen Turai ta yamma. Sabo da haka na hakake, a sakamkon ci gaba da ake samu wajen yin hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika a fannin tattalin arziki da ciniki, tabbas ne, jama'ar Afrika za su kara samun moriyarsu." (Halilu) 1 2 3
|