Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 21:25:21    
Kwararren kasar Sin ya karyata surutun banza na wai  darikar sabon mulkin mallaka na kasar Sin

cri

A kwanakin nan, wasu kafofin watsa labaru na kasashen Turai ta yamma sun nuna ra'ayin kuskure a kan hadin guiwar da ake yi tsakani Sin da Afrika da mataki da kasar Sin ta dauka wajen ba da gudummowa ga kasashen Afrika, wai kasar Sin tana yalwata hulda da ke tsakaninta da kasashen Afrika domin gurbataccen man fetur da sauran makamashi, kuma wai kasar Sin tana gudanar da darikar sabon mulkin mallka. Yayin da Malama Zhang Juan, wakiliyar gidan rediyo kasar Sin ta kai ziyara ga Malam Wang Hongyi, mataimakin shugban ofishin nazarin harkokin Afrika da na kudancin Asiya da gabas ta tsakiya na cibiyar nazarin harkokin duniya ta kasar Sin don jinta bakinsa a kan wannan, sai ya karyata wannan ra'ayin kuskure. Ya ce, "kasashen Afrika sun sami fa'ida sosai daga wajen hadin guiwar da ake yi a tsakaninsu da kasar Sin ta fuskar aminci. Ta haka sun rage dogara da wasu masana'antun kasashen Turai ta Yamma, kuma sun kara kubutar da kansu daga sarrafawa da wadannan masana'antu ke yi musu har cikin dogon lokaci. Sabo da haka kasashen Turai ta yamma sun yi kishi, har ma wasu kafofin watsa labarunsu sun ginginta magana don shafe kashin kaji ga dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika, har ila yau sun dora wa kasar Sin "sabon mulkin mallaka."


1  2  3