Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 21:25:21    
Kwararren kasar Sin ya karyata surutun banza na wai  darikar sabon mulkin mallaka na kasar Sin

cri

A gun taron manema labaru da aka shirya a kasar Masar a ran 18 ga wata, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin wanda ke yin ziyara a Afrika ya karyata surutun banza na wai darikar sabon mulkin mallaka na kasar Sin. Ya ce, ko kusa, ba a iya dora wa kasar Sin darikar sabon mulkin mallaka ba. Malam Wang Hongyi shi ma yana ganin cewa, irin wannan surutun banza da wasu tsirarrun mutanen Turai ta Yamma ke yi ba shi da makama. Ya ce,"da farko, a fannin siyasa, alamar musamman ga darikar sabon mulkin mallaka ita ce yin shisshigi cikin harkokin gida na sauran kasashe, da dora wa sauran kasashen burinsa karfi da yaji, da kuma neman moriyarsa ba ji ba gani a fannin siyasa da tattalin arziki da diplomasiya. Amma kullum kasar Sin tana nacewa ga bin ka'idojin zaman daidaici tsakanin kasashe manya da kanana, musamman ma ko da yaushe kasar Sin tana gudanar da manufofin diplomasiyarta na rashin tsolma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, don haka ta sami yabo daga kasashen Afrika gaba daya. A zahiri ne wannan ya banbanta harkokin waje da kasar Sin ke yi daga harkokin waje na kasashen Turai ta yamma. Sabo da haka ba mai yiwuwa ba ne a dora wa kasar Sin "darikar sabon mulkin mallaka", sa'an nan kuma irin wannan surutun banza ba zai sami amincewa daga wajen kasashen Afrika da sauran kasashe masu tasowa ba. A fannin tattalin arziki, kasar Sin tana aiwatar da manufar ciniki don moriyar juna da cin riba cikin daidaici, tana nuna biyayya sosai ga ka'idojin ciniki na kasa da kasa, yayin da take yin ma'amalar tattalin arziki a tsakaninta da kasashen Afrika, kuma tana bunkasa huldar ciniki a tsakaninsu bisa ka'idojin kasuwanni da aka amince da su a duk duniya. Ta haka kasar Sin ta kawo wa jama'ar Afrika fa'ida sosai."


1  2  3