Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 14:23:27    
Hanyar dogo ta Qingzang, wato hanyar dogo ce da ta fi tsayi daga leburin teku a duniya

cri

To, mene ne wannan hanyar dogo za ta kawo wa tudun Qingzang da mutanen da suke da zama a kan tudun? Mr. Nima yana da zama a wani kauyen da ke karkarar birnin Lhasa. A da, ya kan ji damuwa wajen sayen takin zamani. "A lokacin bazara, lokacin da ake bukatar takin zamani domin noman shuke-shuke, ba za mu iya samu ba domin ba a iya kawo mana takin zamani ba. Amma yanzu, ba zan ji damuwa ba domin za a iya kawo mana takin zamani da jirgin kasa. "

Nima ya gane cewar hanyar dogo ta Qingzang za ta kawo musu wasu sauye-sauye kan abubuwa da yawa ba ma kawai takin zamani ba. Mai yiyuwa ne za su iya ganin mutane da yawa na sauran wuraren kasar Sin har mutanen kasashen waje.

A da, akwai wuyar shiga jihar Tibet, farashin yawon shakatawa a jihar Tibet ya yi tsada kwarai. Idan mu Sinawa muka so zuwa jihar Tibet domin yawon shakatawa, yawan kudin da za mu kashe zai fi yawan kudin da muke kashewa domin yawon shakatawa a wasu kasashen waje yawa. Madam Liang Yuan wadda ke kula da harkokin yawon shakatawa a wani kamfanin yawon shakatawa tana ganin cewa, bayan da aka kaddamar da hanyar dogo ta Qingzang, irin wannan halin da ake ciki yanzu zai samu sauye-sauye. "Idan an dauki jirgin kasa an je jihar Tibet domin yawon shakatawa, farashin yawon shakatawa zai yi arha. Sannan kuma, za a iya sabawa da yanayin tudun Qingzang a sannu hankali. Bugu da kari kuma, akwai wurare masu kyaun gani da yawa a kan hanyar dogo daga birnin Xining na lardin Qinghai zuwa birnin Lhasa na jihar Tibet. Ba a iya ganin wadannan wurare masu kyaun gani ba a cikin jirgin sama."

Hukumar da abin ya shafa ta yi hasashen cewa, bayan kaddamar da hanyar dogo tun daga ran 1 ga watan Yuli mai zuwa, yawan fasinjojin da wannan hanyar dogo za ta dauka zai wuce dubu dari 9. Za a yi sufurin kayayyakin da jihar Tibet take bukata da jiragen kasa.(Sanusi Chen)


1  2  3