Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 14:23:27    
Hanyar dogo ta Qingzang, wato hanyar dogo ce da ta fi tsayi daga leburin teku a duniya

cri

A mako mai zuwa, wato tun daga ran 1 ga watan Yuli, hanyar dogo ta Qingzang, wato hanyar dogo da ta fi tsayi daga leburin teku a duniya za ta fara yin gwajin sufurin fasinjoji. Sabili da haka, za a kawo karshen tarihin rashin hanyar dogo da ke hade jihar Tibet mai cin gashin kanta da sauran wuraren kasar Sin kwata kwata. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku dalilan da ya sa Sinawa suka kau da wahaloli iri iri domin shimfida wannan hanyar dogo da take ratsa tudun Qingzang, wato kololuwar tsaunukan duniya da amfanin wannan hanyar dogo ga mutane wadanda suke da zama a kan tudun Qingzang.

Hanyar dogo ta Qingzang wadda ke hade da birnin Xining, hedkwatar lardin Qinghai da birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kanta tana yammacin kasar Sin. Tsawon wannan hanyar dogo ya kai kilomita 1956, matsakaicin leburin teku na wannan hanyar dogo ya kai fiye da mita 4500. Sabo da haka, an kira wannan hanyar dogo "Hanya ce da ke cikin sararin sama". Kowa ya sani, ana karancin iska, amma hasken rana yana da karfi a kan tudun Qingzang da wannan hanyar dogo ta ratsa. Bugu da kari kuma, kankara tana kasancewa a cikin yawancin lokaci na kowace shekara. Wasu kwararru sun taba daukar cewa ba zai yiyu a shimfida wata hanyar dogo a kan tudun Qingzang ba.


1  2  3