Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 14:23:27    
Hanyar dogo ta Qingzang, wato hanyar dogo ce da ta fi tsayi daga leburin teku a duniya

cri

Mr. Sun Yongfu, mataimakin ministan kula da harkokin hanyoyin dogo na kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Bayan kaddamar da wannan hanyar dogo, za a iya yin amfani da ita wajen yin sufurin kayayyaki da mutane da jihar Tibet take bukata domin neman bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar jihar Tibet. A sa'i daya kuma, sabbin masana'antu za su bulla sakamakon kaddamar da wannan hanyar dogo."

Tun daga shekaru 50 na karnin da ya gabata, Sinawa sun yi aikin shimfida hanyar dogo da ke hade da birnin Xining na lardin Qinghai da birnin Lhasa na jihar Tibet. Amma a wancan lokaci, kasar Sin ba ta samu ci gaban tattalin arziki da fasahohin zamani ba, bayan da aka shimfida wani sashen wannan hanyar dogo daga birnin Xining zuwa birnin Germu, an dakatar da aikin shimfida wannan hanyar dogo. Sai a shekara ta 2001, kasar Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki da fasahohin zamani, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tsaida kudurin ci gaba da shimfida wannan hanyar dogo daga birnin Germu zuwa birnin Lhasa. To, mene ne wahalolin da ake sha lokacin da ake shimfida wannan hanyar dogo ta Qingzang?

Wadannan wahalolin da suka fi tsanani su ne dusar karkara da maganar kiyaye muhalli da rashin iska a kan tudun. Idan ya kasance da dusar kankara, tushen hanyar dogo ba zai iya samun karko ba, wannan zai haddasa hadari ga jirgin kasa. Sannan kuma, domin an shimfida wannan hanyar dogo a kan tudun da ke da tsayi sosai daga leburin teku, za a iya bata muhalli cikin sauki sosai. Sabo da haka, ta yadda za a iya kiyaye muhalli lokacin da ake shimfida wannan hanyar dogo ya zama wata maganar da ke kasancewa a gaban kamfanonin shimfida hanyar dogo. Bugu da kari kuma, ana karancin iska a kan tudu inda ke da sanyi sosai a duk shekara, wannan ma wani kalubale ne ga mutanen da suka shimfida wannan hanyar dogo. Yanzu, bayan da ma'aikatan kamfanonin shimfida hanyar dogo suka yi kokari a cikin wadannan shekarun da suka wuce, an riga an kau da wadannan wahaloli kwata kwata. An kuma gama aikin shimfida wannan hanyar dogo.


1  2  3