Dalili daban shi ne Mr. Bush yana so ta wannan hanya zai bayyana niyyarsa don warware matsalar Iraq . Bayan da aka kafa sabuwar gwamnatin kasar Iraq , hargitsi tsakanin bangarorinrukunoni addini ya kara tsanani , kuma yawan kai farmaki ga sojojin kasar Amurka da ke kasar ya karu . Bugu da kari kuma wasu kasashen da suka shiga yakin suna neman janye jikinsu daga kasar Iraq . A ran 7 ga watan nan , Ministan harkokin waje na kasar Italy ya bayyana cewa , daga wannan wata kasarsa za ta fara rage yawan sojojin kasarsa dake kasar Iraq , kuma a karshen wannan shekara za a janye duk sojojin Italy daga kasar Iraq . A ran 13 ga watan Mr. Bush ya yi jawabi ga sojojin kasar Amurka , inda ya jaddada cewa , kasar Amurka ba za ta yi watsi da kasar Iraq ba .
Masu binciken al'amuran duniya sun bayyana cewa , idan halin da kasar Iraq ke ciki yanzu ya ci gaba da lalacuwa , to , ko shakka babu , manufar Bush kan kasar Iraq za ta gamu da matsaloli a cikin kasar Iraq da kasashen duniya.(Ado ) 1 2 3
|