Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labarin cewa , a ran 13 ga watan nan , Shugaba Bush na kasar Amurka ya isa birnin Bagadaza , hedkwatar kasar Iraq , don yin ziyarar da ba a sanar ba . Wannan shi ne karo na biyu da Mr. Bush ya kai ziyara a Iraq tun bayan da aka gama yakin Iraq a shekarar 2003 , kuma karo na farko ne da ya yi bayan da aka kafa sabuwar gwamnatin kasar Iraq a watan jiya .
A lokacin ziyarar ba zato ba tsamani ta wannan karo , Mr. Bush ya yi shawarwari da Nuri Al-Maliki , firayin ministan kasar Iraq kuma ya yi jawabi ga sojojin kasar Amurka da ke kasar Iraq . Walker Bush ya yi kira ga jama'ar kasar Iraq da su hada kai da sabuwar gwamnatin Al-Maliki don yon kokarin kawo karshen tarzomar zubar da jini . Ya kuma bayyana cewa , kasar Amurka za ta yi kokarin ba da taimako ga sabuwar gwamnatin don samun nasara .
1 2 3
|