Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-15 15:56:55    
Ina Dalilin da ya sa shugaba Bush na kasar Amurka ya kai ziyara a kasar Iraq ba zato ba tsamani?

cri

Bisa labarin da aka bayar , an ce , A ran 12 ga watan nan , Mr. Bush ya yi shirin yin shawarwari da Maliki, firayin ministan kasar Iraq ta hanyar talabijin , daga baya ba zato ba tsamani ya sauya shirin kuma ya tsai da kudurin kai ziyara a birnin Bagadaza don ya gana da Mr. Al-Maliki . Ina dalilin da ya sa ya yi haka ? Masu lura da al'amuran duniya suna ganin cewa , dalili na farko shi ne don nuna goyon bayan gwamnatin Al-maliki , saboda Mr. Al-Maliki firayin ministan ne da kasar Amurka ta zaba . A wannan rana yayin da Mr. Bush ya gana da Mr. Al-Maliki , ya ce , kasar Amurka za ta cika alkawarin farfado da kasar Iraq .

Dalili na biyu shi ne don kara yawan goyon bayan ra'ayoyin jama'a da samun kuri'un goyon bayan Jam'iyyar Republic . A cikin wasu watannin da suka shige , jama'ar kasar Amurka su kan kushe manufar Bush kan kasar Iraq . Wani sakamakon binciken ra'ayoyin jama'a da aka yi ya bayyana cewa , mutane kashi 59 cikin 100 suna ganin cewa , kasar Amurka ta tayar da yakin Iraq wani kuskure ne . Mutane kashi 54 cikin 100 suna ganin cewa , kasar Iraq filin yaki ne da ba a iya ganin nasara ba . Ba mai yiwuwa ba ne za a kafa wata gwamnatin dimokuradiya a can ba .


1  2  3