Dayake rawayen kogi na da tsawo sosai , kuma wuraren da ya ratsa na da yawan gaske, shi ya sa ya kan sauya yanayinsa wajen yanayin sararin samaniya da lokatai daban daban da dai sauransu, a ganin malama Liu Shuqin , irin wadannan bambance-bambance da aka samu su ne farin ciki ko bakin ciki da kogin ya yi, a wajenta, rawayen kogi na da rai. Ta ce, a kowane karon da na tafi zuwa rawayen kogi, sai na sami bambance-bambancen da na ji na gani, har ma na ji cewa, ni da rawayen kogi muna haduwa a gu daya, in na kalli rawayen kogi a shirye-shiryen TV ko kuma zane-zanen da na yi dangane da kogin, sai na yi farin ciki sosai, na ji ina kaunarsa sosai da sosai.
Yanzu, Liu Shuqin ta sami lambobin yabo da yawa, kuma ta taba samun damar yin nunin zane-zanenta a kasar Faransa. Ta ce, kodayake na sami wasu sakamako, amma mafari ne gare ni wajen cim ma burin samun sakamako a fannin fasahohi, zan kara kokarina wajen yin zane-zane.(Halima) 1 2 3
|