Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-14 17:32:43    
Wata shaharariyyar mai yin zane-zane ta kasar Sin

cri

Mutanen kasar Sin sun kira rawayen kogi da cewar kogin mahaifiya. Mafarinsa yana daga fiffitattun matsauni na Qinhai-Tibet, ya malala daga yamma zuwa gabas a kasar Sin. Wuraren da ke bakunan rawayen kogi su ne wuraren soma wayin kai na zamani aru aru na kasar Sin, masu fasahohi na dauloli daban daban da na zamani daban daban na kasar Sin sun bayyana kyakkyawan kogi da karfinsa ta hanyar fahimtar musamman da suka yi. Wata shaharariyyar mai yin zane-zane ta kasar Sin Liu Shuqin ita ma tana daya daga cikinsu.

Ta bayyana cewa, an yi wani nunin zane-zane, kuma an gayyace ni don samar wa nunin nan zane-zanen da na yi, na ji ban burge da kyau sosai ba wajen yin zane-zane, shi ya sa na roki wani mutum da ya mika zanena ga nunin da aka yi, amma ba zato ba tsammani na sami lambar zinariya, da farko, ban amince da wannan ba, na yi tsammani cewa, ko an yi wasa hankali na ne. Kai wannan nasarar farko da na samu ta kara mini karfi sosai wajen yin zane-zane.

An haifi Liu Shuqin a birnin Zhumadian na lardin Henan da ke bakin rawayen kogi. Malama Lui Shuqin ta bayyana cewa, mahaifiyata ita ma ta yi aikin fasaha, tana kaunar fasahohi iri iri sosai bisa tasirin mutanen iyalanta, kuma tana son yin zane-zane, ta taba tattara abubuwa masu kyau da yawa daga ayyukanta domin yin zane-zane.


1  2  3