A shekaru 70 na karshen karni na 20, Malama Liu Shuqin ta sami damar shiga jami'ar Heman don koyon fasahar yin zane-zane, ta yi fatan za ta yi aikin da ya shafi aikin yin zane-zane, amma an aike ta zuwa aiki a wani dakin kula da harkokin al'adu na hukumar al'adu , kodayake aiki na yau da kullum na da yawan gaske gare ta, amma ta yi kokarin samun damar yin zane-zane.
A shekarar 1997, malama Liu Shuqin ta bar aikinta na da, ita da kanta ta tafi birnin Beijing don neman cim ma mafarkinta na yin zane-zane. Ta ce, a shekarar 1997, na shiga wata kolejin koyar da ilmin yin zane-zane na birnin Beijing, muhimman abubuwan da na yi koyi da su su ne batutuwa dangane da rawayen kogi. A cikin shekara da shekaru, ta yi ta yin koyo a fannin nan, kuma tana zane-zane a bakunan rawayen kogi har sau da yawa.
1 2 3
|