Haikalin addinin Buddh mai suna "Ta'er" yana da nisan kimanin kilomita 25 daga kudu maso yammacin birnin Xining, kuma shi ne cibiyar addinin Buddah a yankunan arewa maso yammacin kasar Sin. Haka kuma fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 400. An gina dakuna iri daban daban da yawansu ya wuce 4500, da farfajiya sama da 1000 a cikin wannan haikali. Abubuwan fasaha masu kayatarwa guda uku da ke cikin haikalin nan sun hada da zane-zane da aka yi a kan bangwaye da tulin kayayyakin surfani da kuma furen man girke.
Haikalin "Ta'er" shahararren wuri mai tsarki ne na addinin Buddah. A kan iya gamuwa da 'yan addinin Buddah masu biyayya ga addininsu sosai wadanda suka fito daga wurare masu nisa, suke durkusawa a kasa, suke zuwa haikalin nan, suke auna nisan da ke tsakaninsu da Ubanjigi, sa'an nan suke addu'o'i don neman samun alheri. Malama Ma Lin wadda ta fito daga birnin Beijing ta ce, duk wani idan ya sami damar zuwa haikalin "Ta'er", to, tabbas ne, zai murza gwangwanin katako da aka rubuta nassin addinin Buddah a kan jikinsu, ya yi addu'a don kara neman samun alheri. Ta bayyana cewa, "Ina sha'awar al'adu irin daban. A nan ne, na fahimci ainihin al'adun addinin Buddah sosai, haka nan kuma ina sha'awar tsabi'ar musamman da ake bi a wurare daban daban. Ba safai a kan ga irin wadannan 'yan addinin Buddah masu biyayya ga addininsu sosai a sauran wurare na duniya ba. "
Jama'a masu karatu. Idan kun sami damar zuwa birnin Xining don yin yawon shakatawa, to, tabbas ne, birnin zai shaku cikin zukatanku sosai. (Halilu) 1 2 3
|