Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-13 16:29:18    
Birni mai sanyi da ake kira Xining a kasar Sin

cri

Tudun Qinghai-Tibet na kasar Sin tudu ne mafi tsayi a duniya. Masanan ilmin labarin kasa da masu tafiye-tafiyen yin bincike da yawa sun dauki wannan tudu bisa matsayin wurare uku da ke kuriyar duniya masu tsananin sanyi kamar birnin Xining da iyakacin duniya na arewa da na kudu. Yanzu za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan birnin Xining.

Birnin Xining wuri ne da aka samu alamar fatan alheri da ake kira yingying domin wasannin Olympic da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008. Haka nan kuma an ce, birnin Xining wuri ne da aka samu fure mai suna Tulip a Turance wanda shi ne fure da ke alamanta kasar Netherland. Da Malam Luo Yulin, magajin birnin Xining ya tabo magana a kan furen nan, sai ya ce, "ana sanyi sosai a wurinmu, zafin rana ya kan sha banban kwarai a dare da rana, kuma ana samun hasken rana mai yawa. Duk wadannan suna dacewa da fure mai suna Tulip ya girma ya tohu sosai. "


1  2  3