Yanzu, furen Tulip ya riga ya zama abu mai kayatarwa a birnin Xining. A lokacin da ake zafi kwarai a garuruwa da birane da yawa na kasar Sin a watan Yuli da Augusta na ko wace shekara, amma a wannan lokaci, ba zafi kuma ba sanyi a birnin Xining. Malam Wang Jun, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "akwai 'yan yawon shakatawa masu dimbin yawa wadanda suka fito daga kasashen waje wadanda su kan sauka a birnin Xining a lokacin zafi, su more idanunsu da hali mai kayatarwa da ake ciki a birnin, a sa'i daya kuma su ci duniyarsu a yanayi mai kyau. Ba safai a kan sami birnin Xining, wuri da ake kaucewa zafi a kasar Sin da kuma duk duniya ba."
Ban da yanayi mai kyau, masu yawon shakatawa za su kai ziyara a haikalin addinin Buddah da ake kira "Ta'er" cikin Sinanci a karkarar birnin Xining. Yau sama da shekaru 400 ke nan da gina wannan haikali.
1 2 3
|