A cikin kasar Thailand da ke cikin karkashin tasiri da amincewar addini da shekarun sarauta ke kawo mata, kullum sarki Bhumibol yana kan muhimmin matsayi. A karshen karnin da ya wuce, kasar Thailand tana cikin hali mai tsanani, kullum ana yin juyin mulkin soja, da hargitsin tattalin arziki, da kuma gyare-gyaren diplomasiya. A shekarar 1947, wato lokacin da Sarki Bhumibol ya haw kujerarsa ba da dadewa ba, bangaren soja ya yi juyin mulki, wannan shi ne karo na farko da Sarki Bhumibol ya gamu. A cikin shekaru 60 da suka wuce, an yi juyin mulkin sau 19, firayin ministoci 20 sun kafa majalisun ministoci 48 daya bayan daya. Kullum Sarki Bhumibol ya tsaya kan matsayin na masu shiga tsakani kan siyasa, sai dai a lokacin musamman, ya yi sulhuntawa don hana kasar da ta shiga hali mai tsanani, sabo da haka, jama'ar kasar Thailand suna nuna girmama da kauna gare shi, kuma an mai da shi "Mai shiga tsakani na karshe". (Bilkisu) 1 2 3
|