Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-13 15:44:35    
Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand

cri

Ran 9 ga wata, an yi bikin murnar cika shekaru 60 hawan kujerar Sarki na Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand, wanda shi ne Sarkin da ya fi dadewa a kan kujerar sarauta a duniya. Sarki Bhumibol Adulyadej, sarki na karo na 9 ne na daular Bangkok na kasar Thailand, ana kiransa Rama ta 9.

Nufin Bhumibol Adulyadej a cikin harshen Thailand shi ne "karfin yankunan kasa-da babu kamarsa". An haifi Bhumibol Adulyadej a shekarar 1927 a jihar Massachusetts ta kasar Amurka, ya taba karatu a kwalejin Eton ta kasar Ingila, bayan haka kuma sai ya shiga jami'o'in Lausanne da Harvard, don yin karatu kan ilmin aikin injiniya da aikin likita. Ran 9 ga watan Yuni na shekarar 1946, an kashe 'dan uwansa, wato Rama ta 8, bisa gayyatar da muhimman jami'an kasar suka yi masa, Bhumibol Adulyadej ya koma kasarsa domin gaji kujerar Sarki, ana kiransa Rama ta 9, a lokacin, shekarun haihuwarsa ya kai 19. Ya zuwa ran 9 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki, an riga an cika shekaru 60 da Sarki Bhumibol ya gaji kujerar.


1  2  3