Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-13 15:44:35    
Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand

cri


Tun daga lokacin samartakar, Bhumibol Adulyadej yana son wake-wake da kide-kide, musamman ma biyano da sax, ya taba samu digirin daktar wake-wake da kide-kide da kwalejin horarwar wake-wake da kide-kide na kasar Austria ya ba shi. Bayan haka kuma yana iya magana da harsunan kasashen waje 7 sosai, kuma matsayinsa na mai zane-zane da daukar hoto ya riga ya kai na sana'a. Har zuwa karshen karnin da ya wuce, yawan digirin girmamawa da Sarki Bhumibol ya samu daga jami'o'i daban daban na duniya ya kai 136, haka kuma ya zama mutum da ya samu digirin girmamawa mafi yawa a duniya.

A ko wace shekara, Sarki Bhumibol zai yi amfani da kudi da yawa daga kudin da gwamnatin kasar ta bayar wa sarauta, domin gina ayyukan samar da ruwa, da gina tashar lantarki, da kuma bunkasa aikin noma, da dai sauransu. Sabo da taimakon da Sarki Bhumibol ya yi wajen fannin aikin noma, ran 26 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki a kasar Thailand, Mr. Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya ba shi lambar yabo ta Hukumar raya kasa ta majalisar Dinkin Duniya.


1  2  3