Bisa shirin da kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin suka tsara, an ce, za a ba da ilmin Olympic tsakanin matasa miliyan dari 4 a duk yankin kasar Sin a shekarar da muke ciki, domin haka, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin za ta kafa makarantu fiye da 500 wadanda abin koyi ne a fannin ba da ilmin Olympic a duk kasar a wannan shekara.
Ainihin Olympic shi ne aikin ba da ilmi. Matasa su ne makomar duniyarmu, haka kuma makomar Olympic. Ba da ilmi tsakaninsu yana da muhimmanci sosai a fannin bunkasuwar wasannin Olympic da zaman al'ummar kasa. Kamar yadda shugaban makarantar midil ta 9 ta Beijing Mr. Ma Baosheng ya ce, wannan dukiya ce mai daraja: 'za mu ba da kayayyakin tarihi a fannin ba da ilmin Olympic ga wasannin Olympic na Beijing ta hanyar kafa makarantu wadanda abin koyi ne a fannin ba da ilmin Olympic. Za mu ba da gudummowarmu ga kasar Sin da Beijing da kuma dukan wasannin Olympic.'(Tasallah) 1 2 3
|