Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-02 19:42:15    
Wasannin Olympic na Beijing ya dora muhimmanci kan ba da ilmin Olympic

cri

Jama'a masu karatu, kafin shirinmu na yau, za mu gabatar muku babban ra'ayi na Olympic, babban ra'ayin Olympic shi ne 'matasa da zaman lafiya'. Har kullum kwamitin wasannin Olympic na duniya da hukumomin biranen da suka shirya wasannin Olympic sun mai da hankulansu kan ba da ilmi da tasiri kan matasa, sun fi dora muhimmacin kan ya da babban ra'ayin Olympic tsakanin matasa. Kowa yana sanin cewa, za a yi wasannin Olympic a kasar Sin a shekarar 2008 a karo na farko, yaya kasar Sin, musamman ma birnin Beijing ya ba da ilmin Olympic a tsakanin matasa? A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku halin da ake ciki a wannan fanni.

A ran 6 ga watan Disamba na shekarar 2005, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin sun hada kansu, sun tsara 'shirin ba da ilmin Olympic tsakanin 'yan makaranatar firamare da na midil don wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008', sun kuma gabatar da makarantu 20 na Beijing, wadanda abin koyi ne a fannin ba da ilmin Olympic. Makarantar midil ta 9 ta Beijing tana daya daga cikin wadannan makarantu 20. Yanzu 'yan makarantar nan sun gabatar mana da yadda aka ba da ilmin Olympic a wannan makaranta.'a gun bikin daga tutar kasar da aka saba shiryawa a ko wane mako, yanzu mu 'yan makaranta mun ba da lacca game da ilmin wasannin Olympic. Ko wane aji ya ba da irin wannan lacca sau daya a ko wane mako, dukan 'yan makarantar suna da damar ba da lacca. Ta haka mun tattara ilmin wasannin Olympic, mun fi koyon ilmi, in an kwatanta da ilmin da malamanmu suka koya mana. Sa'an nan kuma, mun yi taro a ko wane mako, inda a kan ba da irin wannan ilmi.'


1  2  3