Ban da ba da lacca kuma, makarantar midil ta 9 ta Beijing ta tafiyar da harkokin ba da ilmin Olympic a jere. Saboda wadannan harkoki, 'yan makarantar sun san ilmin wasannin Olympic da yawa, sun kuma kara nuna sha'awa sosai kan wasannin motsa jiki da wasannin Olympic. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, sannu a hankali sun tabo wasu muhimman abubuwa na ra'ayin Olympic. Cheng Meng, 'yar makarantar, ta gaya wa wakilinmu cewa,'ina tsammanin cewa, ra'ayin Olympic ba ma wasu ilmin da muka sani ne kawai ba, har ma ya sa hannu cikin zaman rayuwarmu ta yau da kullun. Ga misali, kara kai matsayi mai tsawo da kara sauri da kuma kara samun karfi' wato'Higher, Swifter, Stronger' a Turance.A ganina, wannan ya nuna karfin gwiwa na mutum. Na taba ba da lacca mai lakabi haka 'na iya daidaita kalubalen da nake fuskanta', na nuna karfin gwiwa a lokacin da nake fuskantar matsaloli da kalubale.'
Ban da 'yan makarantar midil ta 9 ta Beijing, sauran makarantu wadanda abin koyi ne a fannin ba da ilmin Olympic sun tafiyar da harkoki iri daban daban masu ban sha'awa. Kwamitin ilmi na Beijing ya kuma tsara wani shiri, zai zabi makarantu 200, wadanda za su yi cudanya da kwamitocin wasannin Olympic na kasashe da yankuna misalin 200 da ke karkashin shugabancin kwamitin wasannin Olympic na duniya; a lokacin shirya wasannin Olympic na Beijing, wadannan makarantu za su koyi ilmi game da harsuna da al'adu na kasa ko kuma yankin da suka yi cudanya, a lokacin wasannin Olympic, 'yan wadannan makarantu za su halarci bikin daga tutar kasa da suka yi cudanya a kauyen wasannin motsa jiki na Olympic, za su yi kallon gasannin da kungiyar wakilan wannan kasa za ta yi.
1 2 3
|