Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-01 10:29:08    
Taron ministoci na karo na 2 na dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da kasashen Larabawa yana kokari kan ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin bangarorin nan biyu a dukan fannoni

cri
 

A cikin jawabinsa da ya yi a bikin bude taron, Mr. Musa, babban sakataren kawancen kasashen Larabawa ya ce,"Ta wannan taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da kasashen Larabawa, za mu yi kokari domin tabbatar da juyewa daga matsayin hadin kai zuwa matsayin kara dankon sabuwar dangantakar abokantaka. Muna fatan za a kara ingantar tushen hadin kai, da kuma habaka filayen hadin kai ta hakikanin hanya."

Shekara nan, shekarar cika shekaru 50 ce da kasar Sin ta kulla huldar jakadanci da wasu kasashen Larabawa. Sabo da haka, wannan taron ministoci ya zama wani muhimmin abu da ke cikin harkar yin cudanya a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.

A cikin shekaru 50 da suka wuce, kyakkyawan hadin kai na gargajiya da aka yi a tsakanin bangarorin nan biyu ya sami ci gaba sosai. Mr. Tang Jiaxuan, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin ya ce,"Ya kamata mu sa himma domin ingiza cudanya bisa matsayai daban daba, domin zama abokai masu nuna amincewa da juna, da karfafa hadin kai wajen tattalin arziki, domin zama abokai masu samu bunkasuwa tare, da kara habaka yin cudanya ta abokantaka, domin zama abokai masu inganci da ke kasancewa tare da yi zaman jituwa ko da yake sun sha bamban a fannin wayin kai, da kuma kara daidaituwa a cikin harkokin kasashen duniya a dukan fannoni, domin zama abokai masu kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da zaman karko na duniya." (Bilkisu)


1  2  3