Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-01 10:29:08    
Taron ministoci na karo na 2 na dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da kasashen Larabawa yana kokari kan ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin bangarorin nan biyu a dukan fannoni

cri


An sanar da kafa dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da kasashen Larabawa ne, a lokacin da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kai ziyara ga babbar hedkwatar kawancen kasashen Larabawa a watan Janairu na shekarar 2004.

Ran 31 ga watan jiya a gun bikin bude taron, Mr. Tang Jiaxuan, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin ya bayyana cewa, taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da kasashen Larabawa na wannan karo yana da ma'ana sosai wajen ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa. Ya ce,"Dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da kasashen Larabawa ya riga ya zama wani muhimmin tsari kan kara tattaunawa da hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa. Ina fata ta wannan taron ministoci, za a iya ci gaba da ingiza gine-ginen dandalin tattaunawar, da tabbatar da hadin kai a dukan fannoni a cikin shirin kudurin dandalin tattaunawar, da kuma kara jimlata sakamakon da aka samu, da neman hanyoyi da tsare-tsaren hadin kai da bangarorin nan biyu za su iya karba, da kuma kara ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.


1  2  3