Jama'a masu sauraro. Ba ma kawai babbar ganuwa wani gini ne mai girma ba, har ma ta zama shaidar tarihin sauye-sauyen zaman jama'a na kasar Sin har cikin sama da shekaru 2000 da suka wuce. Wasu mutane suna ganin cewa, babbar ganuwa ginshikin al'ummar Sin ce. A idon jama'ar Sin kuma babbar ganuwa tana wakiltar halin al'ummar Sin. Malam Lai Baojia, dan yawon shakatawa na Taiwan ya ce, duk lokacin da ya ga babbar ganuwa, sai nan da nan ya ji alfahari da ita bisa matsayinsa na wani Basine. Ya ce, "babbar ganuwa na wakiltar halin al'ummar Sin, kuma tana wakiltar hikimar Sinawa. Daga wajenta, za a ga tsoffafin abubuwa na can can zamanin da, kuma tana kasancewa a doron duniya bisa halinta mai ban mamaki, to, yaya ba za a yi takama da ita ba?"
Sinawa suna da karin magana cewa, idan wani bai taba zuwa babbar ganuwa ba, to, shi ba namijin duniya ba ne. Ba ma kawai babbar ganuwa tsohon gini ne mai girma a kasar Sin ba, har ma ita tsohon wuri ne na al'adun duniya masu daraja kwarai. Idan kun sami damar zuwa kasar Sin, to, kamata ya yi, ku ziyarce ta. (Halilu) 1 2 3
|