Sinawa suna ganin cewa, babbar ganuwa abar alfahari ce ga jama'ar Sin. Babbar ganuwar tana daya daga cikin manyan ayyuka mafi girma ga tarihin bil-adam, duk duk tsowanta ya wuce kilomita 6,700, tana shimfide kuma tana kwalmade-kwalmade kamar wata babbar mesa da ke kwance a babban yanki a arewacin kasar Sin. Ba ma kawai ita tsohon kayan tarihi na duniya ne mai arzikin al'adu ba, har ma wuri ne mai ni'ima kuma mai kayatarwa har ba safai a kan samu irinsa ba a duniya.
Yau sama da shekaru 2000 ke nan da aka fara gina babbar ganuwa. Ita tsohon aikin tsaro ne da aka shafe lokaci mai tsawon gaske ana yinta tare da shan tulin wahalhalu. To, su wane ne suka yi wannan aiki mai girma kamar haka? Malam Dong Yaohui, babban sakataren kungiyar nazarin babbar ganuwa ta kasar Sin wadda ita ce kungiyar nazarin babbar ganuwa da kare ta ya bayyana cewa, "wadanda suka gina wannan babbar ganuwa a zamanin da, sun kasu cikin rukunoni uku, wato na farko, su ne sojoji, dalilin da ya sa haka shi ne domin yin aikin nan wani babban mataki ne da kasar Sin ta dauka. Na biyu 'yan kwadago ne da gwamnati ta tilasta su. Na uku kuwa masu laifuffuka ne da aka kore su zuwa sansanonin gwale-gwale."
1 2 3
|