Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-30 15:50:02    
Babbar Ganuwa a kasar Sin

cri

An gina yawancin sassan babbar ganuwar ne a kan manyan duwatsu da wurare masu kawo hadari da wuyar zuwa. Don haka an taba cin gajiyarta sosai wajen tsaron kai. Sa'an nan kuma an gina tasmahara da husumiya da sauran wurare masu muhimmanci da yawa a fannin tsaro a kan babbar ganuwar nan. Hafsoshi da sojoji wadanda suka yi gadi a kan babbar ganuwar, sun dogara da ganuwa mai karko wajen murkushe hare-hare da makiya suka kai musu. Idan suka gamu da mahara masu dimbin yawa, to, za su iya hura wuta don nuna alamar zuwansu, ta yadda za a aika musu da karin sojoji masu ba da taimako. Tun bayan da aka gina babbar ganuwar, an sha yin yake-yake masu tsanani da yawa a gindin babbar ganuwa.

Yanzu, ba a mayar da babbar ganuwa bisa matsayin gine-ginen yaki ba, amma ta riga ta zama shahararren tsohon wuri mai ni'ima. Yawan masu yawon shakatawa na gida da waje wadanda ke sha'awar zuwa babbar ganuwa mai girma da hadari don yin ziyara ya kan wuce miliyan 10 a ko wace shekara.

Ba sau daya ba sau biyu ba, budurwa Helena Darcq ta kasar Faransa wadda ke da shekaru 22 da haihuwa a bana ta yi yawon shakatawa a babbar ganuwa, ta bayyana cewa, ko kusa ba za ta manta da ziyara ta farko da ta yi a kan babbar ganuwa ba har duk rayuwarta. Ta ce, "ba zan manta da ziyarar da na yi a waccan rana ba, na ga bishiyoyi da ciyayi masu launin kore shur a kewayen babbar ganuwa wadda ke shimfide kuma ke kwalmade-kwalmade. Lalle, halin yana da kyau kwarai. Abin da ya fi burge ni shi ne yayin da nake hawan kan babbar ganuwa a mataki bisa mataki. Ko da yake da kyar na yi hawa, amma duk da haka na ga ni'imataccen hali mai ban mamaki da ake ciki a babbar ganuwa."


1  2  3