A cikin wani babban gini mai benaye 10 dake cibiyar birnin Wuhan , hedkwatar Lardin Hubei , kamfanin cartoon na Jiangtun yana benaye 3 . Wannan kamfanin an kafa shi ne a shekarar 2000 . Kuma ya riga ya zama daya daga cikin kamfanoni masu karfi . Yanzu ya riga ya wallafa wasannin kwaikwayon cartoon masu yawa . Mr. Zhu Yougan , babban manajan kamfanin ya ce , tun daga farkon wannan shekara an sayar da wasannin cartoon guda 19 ciki har da " Dodon dake birane " da " Al'ajabi mai shan jini " da sauransu . A watan Nuwamba da ya shige , gabobi biyu na Tekun Zirin Taiwan sun hada kansu sun buga cartoon labarin tarihi mai suna "Sabuwar Daular Song " . A shekarar 2005 , wasannin cartoon da Kamfanin Jiangtong ya wallafa sun yaye a kudu maso arewacin kasar Asiya . An kiyasta cewa , ya zuwa karshen wannan shekara yawan wasannin katoon zai kai kusan 100 . Wannan ba a iya ganin saurinsu ba a cikin shekaru biyu da suka wuce . Ma iya cewa , bayan da aka fitar da labarun soyayya a hanyoyin sadarwar internet , wasannin kwaikwayon cartoon sun zama sabon salo mai jawo hankulan mutane .
Gwamnatin kasar Sinta gabatar da sabon tsarin kirkire-kirkire, wannan ba kawai a wajen kimiyya da fasaha ba , har ma a wajen masana'antun al'adu . Yalwatuwar masana'antun al'adu na Lardin Hubei ta sa mutane suka sauya tsohon tunani kuma ta kawo karfin kirkire-kirkire . Alal misali , Kamfanin Jiangtong ya riga ya zama madugu a wajen wallafa sababbin wasannin cartoon a duniya . Amma duk da haka , Mr. Zhu , babban manajan kamfanin ya ce, nan gaba za su mai da hankali kwarai a kan ingancin wasannin cartoon.(Ado ) 1 2 3
|