Kogin Rawaya wato Kogin Huanghe mafari ne na tsofafin al'adun kasar Sin . Duk wadannan sun bayyana kyakkyawa mai jawo hankulan mutanen duniya .
Wu Xiaonu , Wakiliyar Rediyon kasar Sin ta ruwaito mana labari cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , a nan kasar Sin tana mai da hankali sosai kan masana'antun al'adu . Gwamnatocin matakai daban daban suna mai da muhimmanci a kansu . Jama'a na bangarori daban daban suna shiga cikin wannan aikin masana'antun . Yanzu larduna da jihohi na kashi 2 cikin 3 na duk kasar Sin sun gabatar da cewar za su kafa masana'antun al'adu da ya zama babbar masana'antarsu . A cikin shirinmu na yau za mu kai ku zuwa Lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin don binciken abubuwan gaskiya a wajen yalwata masana'antun al'adu .
1 2 3
|