A karkashin tsarin maki 21 na yanzu , idan a farkon gasar makin da bangarori biyu suka samu ya kara bi da bi , to a karshe dai kowa zai ji ba dadi , kuma yawan ba da fasahar wasan zai rage . Yanzu ni ma na yi haka .
Kalmar "Ba dadi" da 'yan wasa na kasar Sin suke cewa ba ta nufin suna yamutse sosai ba . Abin da suke nufi shi ne su da kansu ba su iya sarrafa gasa bisa shirin da suka yi ba . Li Yongbo , babban jami'in ba da horo ga 'yan wasa na kungiyar wakilan kasar Sin ya bayyana halin musamman na sabon tsarin gasar .
Sabon tsarin maki 21 ya kawo wasu dama ga ga
wasu kungiyoyin wasannin kwallon badaminto da wasu 'yan wasa wadanda ba su kai matsayin gaba ba . A cikin gasar mai yiwuwa ne za a ba mutane mamaki . A ganina dalilin da ya sa sabon tsarin ya jawo hankulan mutane , shi ne a cikin gasar za a fitar da wasu abubuwan ba zato ba tsamani . Yanzu tsarin maki 21 ya sa kwallon badaminto ya sami yalwatuwa , mai yiwuwa ne za a ga sakamako kamar na kwallon kafa wanda ba za a iya kimanta sakamakonsa ba .
A cikin shekaru fiye da 50 da suka shige an yi wasan badaminto bisa doka mai tsarin maki 15 . Ba zato ba tsamani an yi mata wasu gyare-gyare . Kafin wasan da aka yi a kasar Japan , lokacin da suke gwajin wasa bisa sabon tsari , ko shakka babu sun gamu da wasu wahaloli . Amma a karshe dai a gun gasasnnin bude wasan , sun sami nasara .
Masu binciken wannan wasaan kwallon badaminto sun ce , doka ana iya gyara ta , amma ba wanda ya iya hana Kungiyar wasan kwallon badaminto ta kasar Sin ta ci nasara.(Ado ) 1 2 3
|