Assalamu alaikum ! Jama'a masu karantun shafinmu na Internet, ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka : Kungiyar wasan kwallon badaminto ta kasar Sin wadda ta ci jarrabawar gyare-gyaren tsarin gasanni .
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , tun daga karshen shekarar 2005 , dokar yin gasar kwallon badaminto ta yi sauye-sauye . Bayan da aka haifar da wannan wasan kwallon badaminto kullum ana yin amfani ne da tsarin maki 15 . Amma yanzu an gyara tsarin daga maki 15 zuwa maki 21 . Ko da ya ke wannan wani karamin sauyi ne , amma ya girgiza 'yan wasan kwallon badaminto . Kungiyar wasan kwallon badaminto ta kasar Sin wadda kullum take kiyaye matsayin gaba a duniya ita ma ta yi kokarin dace da sabon tsarin .
Tun daga ran 27 ga watan Afrilu zuwa ran 7 ga watan Mayu a kasar Japan an yi wasannin kungiya-kungiya masu cin kwafin Thomas da kwafin Uber a shekarar 2006 . Wannan karo na farko ne da aka yi gasannin kwallon badaminto bisa sabon tsarin . Sauye-sauyen tsarin gasanni sun kawo tasiri ga dukannin kungiyoyin wasan kwallon badaminto na kasashe daban daban ciki har da kungiyar wakilan kasar Sin .
1 2 3
|