In an tsaya ana hange daga gindin dutsen Lushan, to, za a ga kayatattun gidaje na zamani da ke cikin manyan bishiyoyi masu launin kore shur a kan dutsen da gajimare ke kewayensu. A shekarar 1885, 'yan mishan na kasar Britaniya sun gina kayataccen gida na farko a kan dutsen nan, ya zuwa yanzu dai yawan irin wadannan gidaje iri-iri masu sifofin kasashe 18 da aka gina a kan dutsen ya wuce 1000. Daga cikinsu akwai gidaje masu sifofi na kasashen Brazil da Italiya da na arewacin Turai da kudancinta da sauransu.
Malama Tang Dongdong, 'yar yawon shakatawa wadda ta fito daga birnin Beijing tana sha'awar irin wadannan gidaje ainun. Ta ce, "kayatattun gidaje na zamani a kan dutsen Lushan ba ma kawai suna da kyaun gani sosai ba, har ma suna wakiltar sigogin musamman na gidajen kasashe daban daban. A duk lokacin da na sami damar sa kafa a dutsen, to, ko shakka babu, zan ziyarci irin wadannan gidaje. A ganina, ban da cewa na more wa idanuna, kuma na iya samun tsoffin labaru da yawa daga wajensu. "
Bayan da aka ziyarci wadannan wurare na dutsen Lushan, in an sami sarari, to, za a iya ziyartar wasu shahararrun tsoffafin haikalai. Alal misali haikali mai suna "Donglin" tsohon haikali ne, yau sama da shekaru 1700 da aka gina shi. Ban da shi kuma, akwai wani haikali daban da ake kira "Bailudong" a cikin Sinanci, inda aka kafa tsoffin bangayen dutse na zamanin dauloli daban daban da yawansu ya kai darurruka. (Halilu) 1 2 3
|